1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Zanga-zanga ta kazance a Bangladesh

Suleiman Babayo ZUD
July 19, 2024

Sabuwar zanga-zangar da ta barke a kasar Bangladesh ta yi sanadiyar mutuwar mutane uku inda aka shafe kwanaki ana kai ruwa rana tsakanin masu zanga-zangar galibi dalibai da jami'an tsaro.

Bangladesh | Dalibai masu zanga-zanga a birnin Dhaka
Masu zanga-zanga a kasra BangladeshHoto: Mohammad Ponir Hossain/REUTERS

Mutane uku sun halaka sakamakon sabuwar zanga-zangar da ta barke a wannan Jumma'a a kasar Bangladesh domin nuna bijire kan matakan daukan ayyukan gwamnati. Mahukunta sun katse layukan wayoyi domin dikile karfin zanga-zangar ta galibi dalibai. Zuwa yanzu fiye da mutane 30 ake hasashe sun rasa rayukansu lokacin zanga-zangar da aka shafe kwabaki ana yi.

Karin Bayani: Bangladesh: An rantsar da Hasina a wa'adi na hudu a jere

Zanga-zangar wacce aka fara makonnin da suka gabata, ita ce mafi girma tun bayan da aka sake zaben Firaminista Sheikh Hasina a karo na hudu a jere, a zaben watan Janairu da manyan jam'iyyun adawa suka kaurace. Dalibai gami da 'yan gwagarmya sun sha alwashin ci gaba da zanga-zangar wadda ta fantsama zuwa sassan kasar.