An halaka mai zanga-zanga a Sudan
January 30, 2022Talla
Jami'an kiwon lafiya a Khartoum babban birnin kasar Sudan, sun tabbatar da mutuwar mutum daya cikin masu zanga-zanga da suka fito kan titunan kasar a wannan Lahadi saboda nuna adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi tare da neman hukunta wadanda suka kashe fararen hula a baya.
Marigayi Mohamed Yousef Ismail mai shekaru 27 a duniya, ya gamu da ajalinsa sakamakon arangama da harsashin jami'an tsaro da ke kokarin tarwatsa dandazon masu boren da ke kokarin cimma fadar shugaban kasar.
Yanzu haka dai kimanin mutane 79 suka mutu, sama da mutane 2,000 sun jikkata wasu na tsare a hannun 'yan sanda tun bayan fara zanga-zangar neman mayar da mulki ga gwamnatin farar hula a watan Oktoba.