Ana ci gaba da zanga-zanga a Yukren
January 31, 2014Talla
A wannan Jumma'a rundunar sojin kasar Yukren ta yi kira ga shugaba Viktor Yanukovych kan ya dauki matakai cikin gaggawa domin kare kasar daga tsunduma cikin gagarumin rikici.
Wannan shi ne karon farko da rundunar ta saka baki kan abin da ke faruwa, yayin da shugaban ya dauki hutu domin a duba lafiyarsa. Sakataren harkokin wajen John Kerry ya nemi shugaban kasar ta Yukren Viktor Yanukovich ya kara mika wuya ga bukatun masu zanga-zanga, domin shawo kan matsalar siyasar kasar.
Kerry ya bayyana haka yayin ziyara a birnin Berlin na kasar Jamus, inda ya gana da ministan harkokin wajen kasar Frank-Walter Steinmeier.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman