1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu daga cikin masu zanga-zanga sun samu raunuka a Sudan

Zulaiha Abubakar
December 26, 2018

Gamaiyar kungiyoyi masu zaman kansu a kasar Sudan sun sanar da mutuwar wani farar hula mai suna Abuzar Ahmed sakamakon muggan raunuka a yayin zanga-zangar kyamar gawmanatin kasar

Unruhen im Sudan - Proteste in Khartum
Hoto: Reuters/M.N. Abdallah

Sanarwar ta kara da cewar akalla mutane 22 ne suke kwance a asibiti cikin mawuyacin hali sakamakon raunukan da suka samu. Zanga-zanga dai ta balle a kasar ta Sudan a makon daya gabata biyo bayan kari a farashin kayan abinci da karancin abinci da ya addabi al'umma a fadin kasar kafin daga bisani masu zanga-zangar suka juye suna kiraye-kirayen shugaban kasar Omar al-Bashir ya sauka daga mulki. A nata bangaren kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa ta tabbatar da mutuwar mutane 37 daga cikin masu zanga-zangar sakamakon harbin jami'an 'yan sanda.