1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ana cikin hali na rudani a Somaliya

February 19, 2021

Jami'an tsaro a Somaliya, sun bude wuta a kan daruruwan fararen hulan da ke zanga-zangar nuna fushi a kan jinkirin da aka samu a kan ranar zabe shugaban kasar.

Somalia Mogadischu | gepanzerter Mannschaftstransporter auf Straße
Hoto: Feisal Omar/REUTERS

Mafusatan 'yan kasar ta Somaliya na bayyana rashin jin dadi ne da halin da kasar ke ciki, inda suke son sai Shugaba Mohammed Abdullahi Farmaajo ya yi sauka daga mukaminsa.

Rahotanni sun ce an sami tashin wata nakiya a kusa da babban filin jirgin sama na Mogadishu babban birnin kasar, inda aka kuma girke wasu motocin sulke a kan manyan hanyoyi.

Rigimar ta faru ne bayan kwashe daren jiya ana jin karar harbe-harben bindigogi a kusa da fadar shugaban kasa.

Babu labarin a kan wadanda suka rasa rayukansu, sai dai mutane na cikin yanayi na fargaba.

Shugaban kasar ta Somaliya Mohamed Abdullahi Farmaajo, na shan caccaka a kan ci gaba da zama kan mulki bayan karewar wa'adinsa. Su ma 'yan majalisar kasar wa'adinsu ya kare tun cikin watan Disamba.

Bisa tsari dai a ranar takwas ga wannan watan na Fabrairu ne aka tsara zaben.