1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Ana cikin mawuyacin hali a asibitin Zirin Gaza

November 13, 2023

Likitoci a Zirin Gaza na ci gaba da nuna damuwa da halin da aka shiga, daidai lokacin da jami'an lafiyar ke cewa babu abinci da ruwan sha gami da wutar lantarki.

Asibitin al Shifa a Zirin Gaza
Asibitin al Shifa a Zirin GazaHoto: Khader Al Zanoun/AFP

Fada tsakanin dakarun Isra'ila da mayakan kungiyar Hamas a wajen asibitin nan na Al Shifah ya tilasta dubban mutane tserewa daga yankin, yayin kuma da wasu bayanan ke nuna cewa akwai daruruwan mutane da ke makale a ciki.

Ana dai ci gaba da nuna damuwa da halin da aka shiga a asibitin, daidai lokacin da likitoci ke cewa babu abinci da ruwan sha gami da wutar lantarki.

Baya ga daruruwan marasa lafiya da ke kwance a asibitin, akwai ma sauran fararen hula da ke fakewa a ciki.

Marasa lafiya ciki har da jarirai da dama ne ke mutuwa saboda halin da aka shiga.

Isra'ila ta ce cibiyoyin lafiya a yankin na kan shelkwatar kungiyar Hamas da aka gina a karkashin kasa.

Hare-hare 4,300 ne Isra'ila ta kaddamar a kan Zirin Gaza a yakin ramuwar gayya da ya biyo harin ba-zata na Hamas wanda ya kashe sama da mutum dubu da 400 a Isra'ila a ranar bakwai ga watan jiya.

Kungiyar Hamas dai kungiya ce da Tarayyar Turai da Amurka da Jamus da ma wasu kasashen duniya ke dauka a matsayin kungiyar ta'addanci.