Ana cin zarafin bil adama a Sudan ta Kudu
October 21, 2014Talla
Babbar kwamishiniyar majalisar a kan sha'anin kiyaye cin zarafin mata a lokacin yaƙi Zainab Hawa Bangura,ta ce a cikin waɗanda irin wannan lamari ya rutsa da su, har da yara ƙanana.
'' Wasu za a yi musu fyaɗen har su mutu,a cikin waɗanda abin ya shafa a kwai mata da maza da yara ƙanana,maza da 'yan mata, kuma kishi 74 na waɗanda ake yi wa fayɗen na da shekaru 18 da haifuwa kana kuma ta ce daga cikin waɗanda aka yi wa fayɗen har da yaro mai shekau biyu.''
A cikin watan Disamba da ya gabata ne yaƙi ya ɓarke a ƙasar ta Sudan ta Kudu tsakanin gwamnatin Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Mashar.Kuma har kawo yanzu babu wani shirin sassantawa da aka cimma.