Ana dab da cika shekaru hudu da yakin Ukraine
February 22, 2026
Wani 'dan jaridar kamfanin dillancin labarai na AFP ya tabbatar da jin karar tashin bama-baman a birnin Kyiv. Kazalika, mai magana da yawun dakarun sojin Ukraine a birnin, Tymur Tkachenko, ya tabbatar da kai hare-haren, inda ya ce makiya sun kai musu farmaki, tare kuma da yin kira ga daukacin al'ummar birnin da su gaggauta neman mafaka a mabuyar da hukumomin kasar suka tanadar ta karkashin kasa.
Karin bayani:Ko za a yi sulhu tsakanin Rasha da Kiyv?
A ranar 24 ga watan Fabrairun 2026, za a cika shekaru hudu da fara yakin Rasha da Ukraine, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane daga kowanne bangare.
Karin bayani:Ukraine ta kai wa Rasha kazamin hari a masana'antar kera makamai
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, na fuskantar matsin lamba daga Amurka wajen amincewa da sabon daftarin wanzar da zaman lafiya a yankin. Kazalika, ana sa ran gudanar da tattaunawa a kwanaki masu zuwa tsakanin Ukraine din da kasashen Turai da kuma wasu kasashen Gabas ta Tsakiya har ma da Turkiyya don lalubo bakin zaren kawo karshen yakin.