1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIngila

Ana dab da kammala zaben Burtaniya mai cike da tarihi

Abdoulaye Mamane Amadou
July 4, 2024

Masu kada kuri'a sun kusa kammala zaben 'yan majalisun dokoki a kasar Burtaniya zaben mai cike da tarihi da kuma ka iya sauya alkiblar siyasar kasar da jam'iyyar Conservativ ta jima tana jan ragamar mulki.

Hoto: Scott Heppell/AP Photo/picture alliance

Nan gaba kadan a wannan yammaci ake kawo karshen zaben 'yan majalisun dokokin Burtaniya, zaben da ke cike da tarhi da kuma daukar hankali.

Karin bayani : Al'ummar Burtaniya na zaben 'yan majalisun dokoki

Ana kallon zaben a matsayin wanda ka iya bude sabon babin siyasa idan har jam'iyyar Labour ta samu galaba kan jam'iyyar Conservatives ta masu ra'ayin rikau, wacce ta shafe shekaru 14 tana jan zare a madafun iko.

Karin bayani : Dubban bakin haure sun shiga Burtaniya

Akalla masu zabe miliyan 46 ne ake sa ran za su kada kuri'a wannan Alhamis domin sabunta kujeru 650 na majalisar dokokin kasar wacce ke da hurumin zaben Firaminista.