Kwararru na tattaunawa gabannin taron AU
July 4, 2019Talla
Shugaba hukumar gudanarwa na kungiyar ta AU Moussa Faki Mahamat wanda ya kaddamar da taron a birnin Yammai ya ce taron zai kasance tarihi game da yadda za a kaddamar da shirin kasuwanci marasa shinge a tsakanin kasashen Afirka a wannan taro. An shirya ranakun Asabar da Lahadi za su kasance ranakun da taron zai kasance a kololuwarsa tare da halarta shugabanni daga sassa dabam-dabam na Afirka. A share daya kuma hukumomin Nijar sun kara karfafa tsaro sakamakon barzanar da ake fuskanta daga 'yan ta'adda na kai hare-hare.