SiyasaGabas ta Tsakiya
Araghchi na kan hanyar zuwa Pakistan
April 24, 2026
Talla
Majiyoyi daga Pakistan sun ruwaito cewa ana sa ran ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi zai isa birnin Islamabad fadar gwamnatin kasar a daren Juma'ar nan, sai dai ba su fayyyace dalilin zuwan nasa da kuma wadanda zai gana da su ba.
A daidai wannan lokaci babban birnin Pakistan na daukar harama domin karbar bakuncin zagaye na biyu na tattaunawa a tsakanin tawagogin Amurka da na Iran, duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da cewa ko Araghchi ya yi wannan tafiya ce domin ganawa da jami'an Washington ba.
A gefe guda shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa zai ci gaba da kara yin hakuri tare da danne girjinsa domin ganin ya cimma jarjejeniyar zaman lafiya da Iran.