Ana dakon jawabin shugaban Madagaska
October 13, 2025
Dubban masu zanga-zanga a birnin Antananarivo na kasar Madagaska sun fara murna bayan sanar da cewa shugaban kasar Andry Rajoelina zai yi jawabi a maraicen wannan Litinin, inda ake sa ran zai sanar da yin murabus.
A karshen makon jiya shugaba Rajoelina da ba a san inda yake boye ba ya yi tir da yunkurin kifar da shi daga madafun iko ba bisa ka'ida ba, bayan da wani bangare na sojojin kasar ya marawa masu zanga-zangar neman ya yi murabus.
Karin bayani: Ana ci gaba da yin zanga-zanga a Madagaska
Duk da san ran da ake yi na shugaban zai jefar da kwallo mangaro, amma gamayyar kungiyoyin matasa ta Gen Z da ta jagoranci zanga-zanga kin jinin shugaban ta yi kiran wani gangami a maraicen Litinin domin ci gaba da yi masa matsin lamba.
Da kimanin karfe bakwai na wannan maraice agogon GMT ne dai shugaban Rajeolina zai yi jawabi daga wani guri da har yanzu ba a sani ba, yayin da wasu majiyoyi suka ce ya fice daga kasar zuwa tsibirin Reunion a jiya Lahadi kuma daga can ya sake daukar jirgi zuwa wata kasa da shi da iyalinsa.