Ana dakon sakamako a kasar Kwango
December 31, 2018Bayan shekaru biyu na kila-wa-kala a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, a karshe an gudanar da zaben shugaban kasa a jiya Lahadi, zaben da kasashen duniya ke sa ran zai sama wa kasar mai fama da rigingimu, sabuwar alkibla.
Majalisar malaman darikar Katholika a kasar, ta ce zaben ya gudana ba tare da gagarumar matsalar da tun da farko aka yi hasashen gani ba.
Sai dai fa bayanai sun tabbatar tashin tashin tashina a wata rumfar zabe a gabashin Kivu ta Kudu, inda ya kai ga mutuwar jami'in dan sanda da baturen zabe gami da wasu mutane biyu.
Kwangon dai a yanzu na gab da mika mulki daga wata gwamnatin zuwa wata, a karon farko tun bayan samun 'yanci daga kasar Beljiyam a shekara ta 1960.
Akwai dai wadanda ke shakkar take-taken Shugaba Joseph Kabila, wanda ya yi kememen mika mulkin a shekarar 2016.