Ana dakon sakamakon zaben Kamaru
October 13, 2025
A galibin yankunan Kamaru an yi zabe cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da wata matsala ba inji babban daraktan hukumar zaben kasar Erik Essouse yayin taron manema labarai bayan zaben shugaban kasa na 12 ga watan Oktoba, inda yake cewa zaben shugaban kasar an yi cikin kwanciyar hankali, a duk fadin kasar da kuma kasashen ketare.
Masu saka ido
Haka zalika bangaren tawagar masu sa ido da suka fito daga kasashen ketare sun shaida wa dw cewa an yi zabe cikin kwanciyar hankali a rumfanan zaben kasar da suka sa ido kuma bisa lura da aka yi wajen tattaro bayanai, akwai bin doka da oda musamman ma mutunta tsarin dimukuradiyya ga 'yan Kamaru.
Duk da cewa an samu rigingimu tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan Issa Tchiroma Bakary a garin Garoua da ke Arewancin kasar, sakamakon jibge jami'an tsaro da aka yi a gidansa bayan ya kada kuri'a inda wasu matasa suka kona wata babban motar jami'an tsaro kurmus, kawo yanzu dai hankula sun kwanta
Akan haka Zakari Yaou Ousseini mataimakin shugabar karamar hukumar Douala na biyu ya yi kira ga matasa da su kaucewa masu neman amfani da su ta mummunar hanya.
Lokacin sanin sakamakon zabe
Ranar 26 ga wannan wata ake sa ran hukumar zaben kasar za ta sanar da sakamakon zabe bayan haka kuma duk dan takara da bai yarda da sakamakon ba, yana iya shigar da kara gaban kotun koli wacce za ta kwashe makwanni tana sauraron korafe-korafen 'yan takara da suka shigar gabanta.
Ana dai ci gaba da tattara bayanai da suka fito daga rumfanan zabe.
Ministan harkokin cikin gida yayin taron manema labarai da ya yi ranar Lahadi bayan kammala zabe cikin gaggawa, ya sake yin gargadi kan wadanda suka yada sakamakon zabe da suka fito daga rumfanan zabe a shafukan sada zumunta ba ya kuma gargadi 'yan jarida da ke bayyana sakamakon ba bisa ka'ida ba.