Yara da aikin soji a Sudan an bayyana su a kan Tik Tok
May 5, 2026
A cikin wani bidiyo da aka wallafa a TikTok, wani yaro dan shekara 12 yana gudu a kan wata hanyar yana rike da bindiga kirar Kalashnikov yana ihun "Allahu Akbar". A bayansa, ana iya ganin gawarwaki zube a kasa na mutanen da aka bindige.
A farkon watan Disamba aka wallafa bidiyon, jim kadan bayan da 'yan tawayen kungiyar RSF suka kwace garin Babanusa na Sudan, abun da ke nuni da cewar an yi hakan tare da yara sojojin. Cibiyar bincike ta 'yan jarida Bellingcat ta sami damar tabbatar da cewa, wasu daga bidiyoyin an dauke su ne kai tsaye a garin na Babanusa.
A 'yan kwanakin nan bidiyo da yawa na yara sojoji a Sudan na yaduwa a shafukan sada zumunta, musamman TikTok. Yawancin yaran ne suka dauki hotunansu ta amfani da kyamarorin wayar hannu, wadanda ake kalllo sau miliyoyi, a cewar Sebastian Vandermeersch, wani dan jarida a Bellingcat. Ya ci karo da wadannan bidiyon ba zato ba tsammani, yayin da yake bincike kan laifukan yaki a Sudan:
Ya ce" Na sami damar shiga shafin TikTok, inda na ga shafukan yanar gizo masu yawa da ke rarraba abubuwan da yaran da aka tilasta wa shiga soja ke yi, wanda miliyoyin mutane suke kallo. Saboda haka ne muka yanke shawarar jawo hankali kan wannan batu, kasancewar irin tasirin da yaran sojojin ke yi a shafukan sada zumunta wani bakon abu ne".
Yakin da aka fara a Sudan shekaru uku da suka gabata, na daya daga cikin bala'o'in jin kai mafi muni a duniya. Kusan mutane miliyan 14 sun rasa matsugunansu, kuma sama da miliyan hudu suna neman mafaka a kasashe makwabta. A cewar Majalisar Dinkin Duniya, kimanin mutane miliyan 34, kashi 65 cikin 100 na yawan al'ummar kasar sun dogara ne da taimakon jinkai. Kamal Eldin Bashir na kungiyar agajin yara ta Save the Children a Sudan ya jaddada cewar yara ne suka fi jin radadin wannan hali...
Ya ce "Tun daga watan Afrilun 2023 ne yara a Sudan ke fama da rikici da kaura da rabuwa da iyalansu da rashin ilimi da kuma rashin samun kulawa da lafiyarsu, ban da rashin abinci mai gina jiki, wanda ke shafar adadi mai yawa na yaran. Matsalar tana da girma sosai. Amma mafi munin bangaren shi ne, yaran da aka raba da iyayensu suna cikin hadarin a daukesu aiki da sauran abubuwa da yawa".
Wadanda suka fi rauni su ne yaran da ba su da rakiya da ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira ba tare da iyayensu ba. A cewar asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), an yi wa kimanin yara 42,000 rijista. Yawancinsu sun rasa iyayensu yayin da suke guduwa ko kuma a lokacin hare-haren bama-bama. Kuma kungiyar RSF ne suka fi daukar irin wadannan yara a matsayin sojoji, in ji Mohamed Othman, shugaban kungiyar bincike ta MDD a kan Sudan:
Ya ce " An san RSF da daukar yara aiki da kuma amfani da su, musamman a wannan yakin. Kuma muna da waddanan bayanan a rubuce, kuma suna amfani da su a fannoni dabam-dabam, ba kawai a wuraren bincike kan hanya ba har ma a matsayin ayyukan leken asiri da sauransu. Kuma wannan babban laifi ne. Daukar yara 'yan kasa da shekara 15 aiki laifi ne a karkashin dokokin ICC kuma duk suna rubuce".
Kungiyar Save the Children ta yi gargadin cewar wadannan yara kanana da ke aikin soja suna karewa da munanan raunuka da kan barsu da tabo har abada. Kididdiga na cewar, har zuwa kaso 50 cikin 100 na yara a Sudan suna fama da matsalar damuwa bayan tashe tashen hankulan kasar.