Ana duba rawa da Faransa ta taka cikin kisan kiyashi na Rwanda
October 24, 2006A kasar Rwanda a yau wani komiti ya fara zamansa zagaye na farko don duba rawa da Faransa ta taka lokacin kisan kiyashi da akayi a kasar a 1994,tare kuma da duba yiwuwar kaita gaban kotun kasa da kasa.
Komitin dake da alhakin yanke wannan hukunci zai saurari shaidu kusan 25 cikin mako guda,ya hada da masana tarihi,kwararru a fannin sharia da manyan jamian soji na tsohuwar rundunar sojin Rwanda ana kuma sa ran zai mika rahotonsa nan da watanni 6.
Cikin wadanda zasu bada shaida a yau har da jakadan Rwanda a kasar Faransa bayan kisan kiyashin,da kuma tsohon shugaban hukumar leken asiri na kasar a shekar 1993 zuwa 1994.
Komitin zai duba zargin cewa kasar faransa ta bada horo da kuma makamai ga wadanda suka aikata kisan kiyashi a Rwanda,inda mutane kusan 800,000 suka rasa rayukansu cikin kwanaki dari na zubda jini a kasar,ta kuma taimakawa wasunsu suka tsere daga kasar.
Kasar Faransa wadda ta aike da dakarunta zuwa kudu masu yammacin Rwanda a makonni karshe na kashekashen a Rwanda ta karyata wannan zargi.