1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ana cikin alhinin rashi da aka yi a hadarin ruwa

June 16, 2023

A Najeriya bayanai na nuna cewa galibin wadanda suka mutu a hadarin ruwa da ya faru a jihar Kwara, mata ne da yaransu da ke kanana. Lamarin ya faru ne a farkon mako.

Hoto: AP/picture alliance

Wani jirgin ruwa kirar katako da ke dauke da sama da mutum 250 da ke kan hanyarsu ta komawa gida bayan halartar wani bikin aure cikin dare ne shi ne ya fashe inda aka rasa mutum 108.

A ranar Alhamis ne dai aka kawo karshen aikin ceton wadanda hadarin ya rutsa da su, kuma tuni aka yi jana'izar wasu daga cikin wadanda suka mutu a gabar kogin da aka yi hadarin.

Yayin da mazauna yankin da lamarin ya faru ke juyayi, sun yi kira ga gwamnatin jihar Kwara, da ta samar musu hanyoyin mota da za su taimak wa zirga-zirga a yankin.

Hukumomi a Najeriyar dai sun ce wannan ne hadarin ruwa mafi muni da aka gani a baya-bayan nan.