Ana fama da zafi mai tsanani a Turai
June 19, 2022Talla
Kasashen Faransa da Spaniya da ma wasu na gabashin nahiyar Turai sun shiga yanayi na zafi mai tsanani a 'yan kwanakin da ake ciki, inda a wasu yankunan ma aka soma ganin ibtila'in gobarar daji.
Zafin da ya haura maki 40 a wasu kasashen, masana sun yi hasashen samun hakan cikin wannan wata na Yuni.
Gobarar dajin ta yi barna musamman a yankin Kataloniya na kasar Spaniya.
Yanayin na zafi dai ba sabon abu ba ne a kasashen na Turai duk da yawan sanyi da ake da shi, to sai dai a wannan karon sun danganta shi da matsalar dumamar yanayi.