1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana fargabar mutuwar manoma a hadarin jirgin ruwa a Najeriya

August 12, 2024

Akalla manoma 16 ne hukumomi ke nuna fargabar sun mutu a arewacin Najeriya, bayan wani hadarin jirgin ruwa da ya auku a jihar Sokoto.

Hadarin jirgin ruwa a arewacin Najeriya
Hadarin jirgin ruwa a arewacin NajeriyaHoto: AP/picture alliance

Masu aikin ceto sun ce jirgin na ruwa kirar katako, ya debo manoma ne da ke kokarin zuwa gonakunsu na shinkafa da safiyar Lahadi. An dai bayyana nauyi fiye da kima a matsayin musabbabin hadarin.

Jimilla dai akwai mutane 36 a cikin jirgin ruwan wanda aka kera domin daukar mutane 15, kuma mutane 19 su ne suka tsira da ransu.

Ya zuwa yanzu, gawar mutum guda ce aka gano a cewar hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA.

Daga cikin fasinjojin jirgin har da mata da kananan yara, inda hankali ya karkata a yanzu a kan yadda za a tsamo mutanen da ake fargabar sun riga mu gidan gaskiya.