Al'umma za su shiga halin tasku a Tigray
November 17, 2020Yayin da kasashen duniya ke ci gaba da matsin lamba akan dirar mikiyar da sojojin Habasha ke yi akan yan aware a yankin Tigray, Firaminista Abiy Ahmed yace farmakin ya shiga matakin karshe kuma gwamnatinsa ta tabbatar da kai wasu sabbin hare hare ta sama a Mekele babban birnin Tigray.
Abiy wanda a shekarar da ta gabata ya sami lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel ya sanar da kaddamar da hari a ranar 4 ga watan Nuwamba wanda yace martani ne kan harin da jam'iyya mai mulki ta TPLF ta kai kan wasu sansanonin soji.
A waje guda kuma sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya yi kakkausar suka akan harin da dakarun Tigray suka kai kan filin jirgin saman Eritrea a Asmara.
A cikin wata sanarwa Pompeo ya jinjinawa Eritrea game da yadda ta nuna halin dattako wanda yace hakan ya taimaka wajen dakile yaduwar rikicin.