1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaRuwanda

Ana gudanar da babban zaben kasa a Ruwanda

July 15, 2024

An bude rumfunan zabe a Ruwanda, inda 'yan kasar za su zabi shugaban kasa da kuma 'yan majalisar dokoki. Shugaba Paul Kagame na yanzu na neman sabon wa'adi a zaben.

Yadda aka fara kada kuri'a a birnin Kigali
Yadda aka fara kada kuri'a a birnin KigaliHoto: Marco Longari/AFP via Getty Images

Miliyoyin 'yan kasar ta Ruwanda ne dai za su kada kuri'a a wannan Litinin, a zaben da ake ganin Shugaba Paul Kagame ne zai iya lashewa inda zai yi mulki wasu shekaru biyar.

Tun a shekara ta 2000 ne dai Paul Kagame ke mulki a Ruwandar, bayan kawo karshen kisan kiyashin kasar da aka yi a shekara ta 1994.

'Yan takara biyu ne ke fafata da Shugaba Kagame, bayan haramta wa wasu fitattun masu sukar lamirin gwmanatinsa da aka yi.

'Yan takarar dai su ne Frank Habineza, jagoran jam'iyyar Democratic Green Party da kuma dan takarar Indifenda Philippe Mpayimana.

Wannan ne karo na hudu da Paul Kagame ke takara a Ruwanda.