Ana gudanar da zabe a Hong Kong
November 24, 2019Talla
Sama da mutum miliyan biyu suka fita rumfunan zabe a Hong Kong, a wannan rana da ake zaben shugabannin majalisun gundumomi.
Zaben na yau ana ganin shi a matsayin mataki ne na raba-gardamar zanga-zangar da aka kwashe sama da watanni biyar ana yi a yankin.
An dai ga dogon layuka a rumfunan zabe dabam-dabam, yayin da aka baza 'yan sandan kwantar da tarzoma saboda ko-ta-kwana.
Sama da 'yan takara dubu da 100 ne ke naman kujerun wakilci 452 na gundumomin da ke a yankin.
Ya zuwa yanzu dai fiye da mutum miliyan guda ne suka kada kuri'a ya zuwa yanzu, a zaben da ake ganin an samu ninkin masu zabe idan aka danganta da wanda aka yi a baya.