Ana gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasa a Iraki
November 11, 2025
Talla
‘Yan kasar Iraki na kada kuri’a domin zaben sabbin ‘yan majalisa, a zaben da Amurka da Iran; manyan kasashe masu tasiri a yankin ke sa ido sosai a kansa.
Zaben na ranar Talata na gudana ne a lokacin da Irakin ke fama da matsalolin cin hanci da lalacewar hanyoyi da tabarbarewar yanayi na ayyuka, duk da dan natsuwar da ta samu a ‘yan shekarun baya.
Fiye da masu zabe miliyan 21 ne suka yi rajista domin zabar ‘yan majalisa 329 daga cikin ‘yan takara sama da 7,700, yayin da kasar ke ci gaba da farfadowa daga tasirin yake-yake bayan kifar da gwamnatin marigayi Shugaba Saddam Hussein.