Ana iya jinkirta kada kuri´a kan kudurin kwamitin sulhu akan Koriya Ta Arewa
October 14, 2006Talla
Duk da dan sassaucin da suka nuna Rasha da Sin sun fara nuna wata adawa wadda ka iya janyo jinkiri a kuri´ar da za´a kada yau akan wani kudurin kwamitin sulhun MDD wanda zai tanadi sanyawa KTA takunkumi saboda gwajin makamin nukiliya da ta yi. Jakadan Amirka a MDD John Bolton ya ce kwaskwarimar da gwamnatocin Mosko da Beijing suka nema da a yiwa daftarin kudurin, wani abu ne na fasaha saboda haka ana iya ci-gaba da kada kuri´ar a yau asabar kamar yadda aka tsara. To amma jakadan Sin a MDD Wang Guangya ya ce har yanzu ba´a cimma wata yarjejeniya ba. a yau kasashe 5 masu ikon hawa kujerar naki a kwamitin sulhu da Japan zasu gana gabanin zaman taron membobi 15 na kwamitin wadanda zasu tattauna game da canje canjen da za a yiwa daftari kudurin. Daftarin baya bayan nan ya nemi KTA da ta lalata dukkan makamanta na nukiliya to amma bai tanadi daukar matakan soji kanta ba.