Ana iya komawa taron kasashe 6 kan shirin nukliyar Koriya Ta Arewa a bana
November 1, 2006Talla
Ministan tsaron Rasha Sergey Ivanov ya ce ana iya komawa ga shawarwarin nan na kasashe 6 kan shirin nukiliyar KTA a cikin wannan shekara. A cikin hira da wani gidan telebijin mista Ivanov ya ce watakila China zata karbi bakonci taron. Jim kadan gabanin haka wani babban jami´in KTA ya nuna shirin kasarsa na komawa ga sabbin shawarwarin. To amma ma´aikatar harkokin waje a birnin Pyongyang ta ce za´a yi haka bisa sharadin cewa za´a tattauna game da kawo karshen takunkuman kudi da Amirka ta sanyawa KTA. Gwajin makamin nukiliya da KTA ta yi a farkon watan oktoba ya kara dagula wannan rikici, wanda hakan ya kai dora mata takunkuman kwamitin sulhun MDD. Tun a bara ne aka katse zaman shawarwari na kasashen 6 da suka hada da kasashen Koriyawa biyu da Amirka da Rasha da Sin da kuma Japan.