1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ana jimamin rasuwar shugaban sojin Najeriya

May 22, 2021

A Najeriya an yi jana'izar babban Hafsan sojin kasa na Najeriya Janar Ibrahim Attahiru da wasu sojoji guda 10 da suka rasu a hatsarin jirgin sama da yammacin ranar Jumma'a a Kaduna.

Nigeria General Ibrahim Attahiru ist gestorben
Hoto: AFP/Getty Images

 Janar Lucky Irabor shi ne babban hafsan sojojin kasar ya kuma shaida wa DW cewwa mutuwar ta zo musu a matsayin labari mara dadin ji, amma dabi'ar da Janar Attahiru ya rayu da ita abu ne da  rundunar soja ke alfahari da shi. Sanarwar da sojojin Najeriya suka fitar sun ce jirgin da ke dauke da sojoji 11 ya kife ne a kusa da filin jirgin sama na Kaduna a yayin da yake kokarin sauka a sakamakon yanayi mara kyau da ya ci karo da shi. A watan Janairun da ya gabata ne dai ne Shugaba Buhari ya nada marigayi Janar Attahiru shugaban sojojin kasa a lokacin da ya sauya manyan hafsoshin sojin kasar, a wani mataki na kara inganta samar da tsaro a kasar da rashin tsaro ya yi mata dabaibayi.