Ana juyayin mutuwar yara a Gambiya
October 11, 2022An gudanar da addu'o'i na musamman ga yara 69 wadanda suka rasa rayukansu bayan shan wani gurbataccen maganin tari da aka shigo da shi kasar daga Indiya. Shugaba Adama Barrow na kasar ta Gambiya ya ba da dokar dakatar da lasisin shagunan da suka sayar da maganin da ma masu shigo da su daga ketare.
Rashin ingantattaun wuraren gwaji da kasar Gambiya ke fama da shi ya haddasa bata lokaci kafin hukumomin lafiya su gano inda matsalar take. Alasan Kamaso guda ne daga cikin iyayen da suka rasa ‘ya‘yansu, ya rasa yaronsa dan shekaru biyu bayan ya sha maganin na tari. Ya kuma ce mutuwar yaronsa da ma sauran yaran ba abin yafewa ba ne.
Da farko likitoci suna ta bai wa yaran magunguna da ba su dace da ciwon ba kamar na Maleriya da Asma da Sankarau da dai sauran su, kafin daga bisani hukumomin su gano ciwon koda ne bayan daukar samfurin jini da suka kai kasar Senegal domin zurfafa bincike.
Abdoulie Jawo, mahaifi ne da ya damu da lafiyar dansa da ma sauran yaran.
''Da zarar ba ka da lafiya inda kake fara tunani shi ne wurin da ake duba lafiya, amma abu ya kai munzalin da za ka je asibiti amma da kyar ka samu maganin da zai magance maka matsalarka. Galibi asiboti sukan tura marasa lafiya shagunan sayar da magunguna ne domin su saya. To idan wadannan shaguna da muka dogara da su bayan asiboticin su ne wadanda ke sayar da gurbatattun magunguna, lallai ko akwai damuwa.''
‘Yan Gambiya dai sun fito kwansu da kwarkwatarsu domin nuna goyon baya da alhini da ma addu'o‘i a kan wannan al'amari, da ma kira ga gwamnati a kan a zo a yi bincike a kuma hukunta masu laifi.
Kungiyoyin fararen hular kasar su ma sun mika kiransu ga kungiyar lauyoyi ta Gambiya da ma sauran lauyoyin masu zaman kansu da su ba da taimako ga iyayen yaran wurin daukar mataki a kan sakacin gwamnatin.