1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana kace-nace kan bunkasar tattalin arzikin Najeriya

Uwais Abubakar Idris AH(AMA)
November 26, 2024

Al'ummar Najeriya na kace-nace kan bayanan da hukumar kididiga ta kasar ta fidda da ke nuna cewa tattalin arzikin kasar ya bunkasa da kashi 3.46 a zango na uku na wannan shekara.

Shugaban Najeriya Bola Ahemd Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahemd Tinubu Hoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Bayanan samun bunkasar tattalin arzikin Najeriyar da kashi 3.46 a zango na uku na wannan shekara da hukumar kididiga jama'a a Najeriya ta fitar ya haifar da cece-kuce. Ci-gaban da aka samu ya zarta wanda aka samu a shekarar da ta gabata da kaso 2.5 a zango na uku na shekarar 2023, kuma tuni ya haddasa martani daga masanan tattalin arziki kamar su Abubakar Ali da ke bayyana cewa. "Abin dubawa shi ne yawancin karin da aka samu na ci gaban tattalin arzikin Najeriya da kusan kaso 54 cikin 100 ya fito ne daga harkokin da suka shafi biyan bukatun yau da kullum, idan ka duba, ba gundarin abin da za a yi murnar cewa tattalin arzikin kasar ya karu ba ne''. 

Karin bayani :Bankunan Najeriya sun samu gagarumar riba

Wannan habakar tattalin arzikin Najeriya ya haifar da murna da zumudi daga bangaren gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ganin cewa sashin da ba na man fetur ba ne ya taimaka ga samun bunkasuwar da tattalin arzikin kasar ya yi. Amma wasu 'yan Najeriya na nuna shakku kan ci gaban, saboda suna korafin ba su gani a kasa ba, duk da yake Dr Isa Abdullahi masanin tattalin arzikin Najeriya cewa yake. "Abin da ya sa daidaikun mutane ba za su fara samun saukin rayuwa ba, sai an yi ta yadda wannan ci gaban zai bai wa talaka sauki rayuwa, kamar abinci da igancinsa da ganin sauyi kan irin suturar da yake sakawa."

Dan Najeriya na kirga kudi Hoto: KOLA SULAIMON/AFP/Getty Images

Karin bayani : Najeriya na kokarin ceto darajar Naira

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana iyakar kokarinta na rage radadin talauci ga alummar kasar, kamar yadda ministan kudi da tattalin arzikin Najeriyar Wale Edu ya sanar. "Abu mai muhimmanci a yanzu shi ne farashin kayan abinci ya sauka, kuma wannan na kan hanya ta yadda za a samar da abinci a wadace kuma mai sauki". Shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba a kokarin da yake na tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasar.