1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaFaransa

Faransa: Kila wa kala kan dorewar sabuwar gwamnati

October 13, 2025

Sa'o'i kadan bayan kafa subuwar gwamnati a Faransa, 'yan adawa sun dau alwashin hanata yin tasiri ta hanyar gabatar da kudurin yi mata yankan kauna.

Sebastien Lecornu, sabon firaministan Faransa
Sebastien Lecornu, sabon firaministan FaransaHoto: Stephanie Lecocq/AFP

Sabon firaministan Faransa Sebastien Lecornu ya bukaci ministocinsa da suka fara aiki a ranar Litinin da su ajiye burikansu a gefe domin shawo kan rikincin siyasa da kasar ta fada, yayin da sabuwar gwamnatin da ya kafa ke fuskantar barazanar yankan kauna muddin ba ta amince da bukatotcin 'yan majalisa na bangaren masu ra'ayin gurguzu ba.

A gobe Talata sabuwar majalisar ministocin ta Faransa za ta gudanar da zamanta na farko a birnin Paris, inda gwamnati za ta gabatar da daftarin kasafin kudi guda biyu da za a gabatar wa majalisar dokoki a cikin gajeren lokaci.

Karin bayani: Faransa ta shiga wani wadi na tsaka mai wuya a siyasa

Sai dai tun tuni shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin Faransa na bangaren jam'iyyar LFI Jean-Luc Melanchon ya yi hasashen cewa babu shakka wannan sabuwar gwamnati ita ma za ta fadi kamar wadanda suka gabaceta, yana mai cewa 'yan majalisa na bangaren masu ra'ayin gurguzu za su amince da kudurin yanke mata kauna da ya gabatar a safiyar yau.