Ana kokawa da kotun ICC Afirka
November 4, 2016Kasashen Afirka da suka sanar da ficewa daga kotun mai hukunta manyan laifuka dai sun hada da Kasar Gambiya da Burundi da Afirka ta kudu. Kasashen dai sun ba da hujjar cewar akwai laifuka masu yawa da wasu kasashen suka aikata amma ba a dau matakin hukuntasu ba, Ministan yada labarai da sadarwa na kasar Gambiya,Sheriff Baba Bojang, shi ne ya yi jawabin ficewar gwamnatin Banjul daga Kotun ICC ga kuma hujjar da ya bayar"Bayan kammala binciken kwamitin kan yakin Iraki wanda kasar Birtaniya ta yi, kuma rahoton ya samu tsohon firaministan kasar da aikata laifin yaki. Amma kotun ICC ba ta gayyaci firaministan ba, ba su ko tanka masa ba,kana ba su tuhumeshi da aikata laifin yaki ba.Akwai kasashen yamma akalla 30 da suka aikata munnanan laifukan yaki, kan kasashe masu yanci da jama'arsu.Tun bayan kafa kotun ICC, amma babu ko da mutun guda da kotun ta tuhuma da laifin yaki daga kasashen yamma".Sai dai a martaninta babbar mai shigar da kara a kotun ICC Fatou Bensouda, wace ita ma yar asalin kasar Gambiya ce da taba rike mukamin ministan Shari'a, ta musanta nuna banbanci a aikin kotun ta Majalisar Dinkin Duniya.