1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaBangladesh

Ana lissafa kuri'u a zaben Bangladesh

January 7, 2024

Hukumar zabe a Bangladesh ta fara lasafta kuri'u a zaben 'yan majalisar kasa da aka yi a ranar Lahadi, zaben kuma da ya kama hanyar tabbatar da nasarar firaminista Sheikh Hasina a karo na biyar.

Yadda ake kirgen kuri'u a zaben Bangaladash
Yadda ake kirgen kuri'u a zaben BangaladashHoto: Mahmud Hossain Opu/AP Photo/picture alliance

Jam'iyyar adawa ta Bangladesh Nationalist Party wato BNP ta tsohuwar Fimanista Khaleda Zia da kawayenta duk sun tsame kansu daga zaben saboda zargin za a tafka magudi.

Rahotanni sun nunar da cewa sama da mutum dubu 25 ciki har da 'yan adawa jami'an tsaro suka garkame, saboda zargin tayar da husuma.

Sama da jami'an tsaro dubu 800 ne dai hukumomi suka baza don tabbatar da tsanaki lokacin zaben, yayin kuma da aka kebe wasu dubu 700 saboda ko ta kwana.

Gwamnatin Bangladesh din ta zargi 'yan adawa da kokarin tarwatsa zaben, zargin kuma da babbar jam'iyyar adawa ta BNP ta musanta.