1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mmartani kan muhawa tsakanin 'yan takara a zaben Amirka

September 27, 2016

Yanayin siyasa yana kara dumama a Amirka duba da irin mabanbantan ra'ayoyin jama'a a kan muhawarar da 'yan takara a zaben shugabancin kasar.

USA Wahlkampf TV Duell
Hoto: Reuters/L. Jackson

Muhawara ta farko tsakanin 'yan takara a zaben neman shugabancin kasar guda biyu kasurgumin mai arzkin nan Donald Trump na jami'yyar Republican da Hillary Clinton tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar ta Jam'yyar Democrat wacce ke mulki a kasar a halin yanzu, ta samu ra'ayin jama'a daban-daban a cikin da wajen kasar, duba da jaddada kudirin da kowanne dan takara yake tare da neman kuri'ar 'yan kasar in lokacin zabe yazo ita dai Hillari Clinton ta kafa ta tsare kan za ta kara wa ma'aikata albashi tare da farfado da kanannan masa'antu sannan za ta tabbatar da anayin raba dai dai a ribar da aka samu a masana'antu tsakanin wanda duka yake da ruwa da tsaki a kirkiraA daya bangaren Donald Trump fadi yake zai rage wa kamfanoni da masa'antu haraji daga kashi 35 zuwa kashi 15.

Hoto: Reuters/S. Stapleton

Ra'ayoyin mutane daga ko'ina a fadin duniya ga abin da wani dan pansho mai suna Andrei Gerasimov daga kasar Rasha ya nuna sha'awa bisa abin da yake faruwa a Amirka. Daga kasar Koriya ta Kudu wani ma'aikaci mai suna Kim Sang cewa yake Trump yana da tsananin kishin kasa amma yana ganin Hillary Clinton za ta fi cancanta ta shugabanci kasar Amirka.
 
'Yan takara biyun sun yi yi kokarin nuna cancanta da suka yi domin jagorancin kasar ta Amirka, inda Donald Trump yake yi wa Hillary Clinton shagube cewa sama da shekaru talatin tana abu daya, amma sai yanzu ne take da mafita ga matsalolin kasar?

Hoto: Getty Images/AFP/E. Munoz