Ana neman kawo karshen rikicin Mali
July 16, 2014Gwamnatin Mali da 'yan tawayen kasar sun fara tattaunawa a birnin Algiers na kasar Aljeriya da nufin samar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsu. Kungiyoyi shida suka amince da shiga a damasu ciki kuwa har da MNLA da ke fafutukar samar da kasar abzunawa ta kashin kansu.
Wasu daga cikin kungiyoyin sun nemi a ba su kwarya-kwaryar cin gashin kai idan ana so su yi watsi da makamai. Ita ma dai gwamnatin Bamako ta nunar da cewar a shirye take ta dauki duk matakan da suka wajaba domin samar da zaman lafiya a arewacin kasar ta Mali.
Tun lokacin da Shugaba Ibrahim Boubakar Keita ya dare kan kujerar mulkin Mali a watan Agustan 2013, batun tattaunawar zaman lafiya ke tafiyar hawainiya a arewacin kasar.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Suleiman Babayo