Ana nuna damuwa kan dokar amfani da wiwi a Jamus
April 1, 2026
Wasu ministoci daga jam'iyyun CDU da CSU da ke cikin gwamnatin hadaka ta Jamus sun bukaci a sake duba dokar halasta amfani da wani adadi na tabar wiwi da aka amince da ita ashekarar 2024.
Ministar lafiya Nina Warken ta ce wannan mataki kuskure ne, tana mai cewa dokar ba ta hana yara da matasa shiga ta‘ammali da kwayoyi ba. Ta kuma nuna damuwa kan rudun da ta ce ake samu a tsakanin masu shan wiwi domin nishadi da wadanda ke amfani da ita a matsayin magani.
Karin bayani: Kasar Jamus na shirin halarta tabar wiwi
Ministan harkokin cikin gida Alexander Dobrindt ya bayyana dokar a matsayin wadda ta gaza, yana zargin cewa matakin ya habbaka kasuwar bayan fage ta sayar da wiwi tare da karuwar aikata laifuka.
Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da hukumomi ke nazarin tasirin dokar a cikin shekaru biyu da amincewa da ita.