Ana samun galaba kan mayakan IS a Iraki
May 23, 2015Talla
Wani jami'in tsaro da ya zanta da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP bisa sharadin za a sakaye sunansa ya ce yanzu haka dakarun gwamnati ne ke iko da yankin Husaybah kuma sun danna kai don kubutar da lardin Jweibah.
Wannan nasara da sojin Iraki suka samu tare da tallafin sojin sa kai da ke bin tafarkin Sunni da Shi'a a yankin na zuwa ne daidai lokacin da dakarun kawancen da Amirka ke jagoranta a yaki da 'yan IS ke kara matsa kaimi wajen kai hari kan mayakan IS din a Ramadi tun daga jiya Juma'a.