Ana samun nasara a yaki da Maleriya
December 9, 2014Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa zazzabin cizon sauro na maleriya ya ja baya a cikin shekaru 14 da suka gabata idan aka yi la'akari da yawan mutane da ta hallaka a duniya. Sai dai kuma ta yi gargadi kan gibin da ake samu na karancin magungunan wannan cuta da kuma gidajen sauro dake dauke da magani.
Cikin rahotonta na shekara shekara da ta wallafa a wannan Talarar, WHO ko kuma OMS ta ce mutane da ke rasa rayukansu sakamakon kamuwa da Maleriya sun ragu da kashi 47 daga cikin 100 tsakanin shekarun 2000 zuwa 2013.
A kasashen Afirka dake Kudu da Sahara inda aka fi fama da zazzabin na cizon sauro, an samu raguwar kashi 54 daga cikin 100 na wadanda cutar ke kashewa. Sai dai kuma Hukumar Lafiya ta Duniya ta nunar da cewar kasashen yammacin Afirka dake fama da annobar Ebola na fuskantar barazanar yaduwar cutar ta maleriya.