1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayoyi sun bambanta kan makomar mulki a Chadi

Abdul-raheem Hassan MAB
April 21, 2021

Shugabannin kasashen waje na nuna alhinin mutuwar takwaransu na Chadi Idriss Deby Itno a fagen daga. Sai dai wasu na nuna damuwa dangane da halin da dimukuradiyya ta shiga bayan da dan marigayin ya dare madafun iko.

Tschadische Soldaten bei Rückkehr aus Mali 13.05.2013 mit Präsident Idriss Deby Itno
Hoto: STR/AFP/Getty Images

Manyan kasashen duniya na ci gaba da nuna alhinin mutuwar Idriss Deby, wanda yawanci ke kallo a matsayin madugun yaki da kungiyoyin ta'addanci a yankin Sahel. Mai magana a madadin Sakataren Janar na MDD Antonio Guterres, wato Stephane Dujarric ya ce rashin Deby tamkar faduwar bango ne da kowa zai ga gibinsa. Ya ce: "Babban Sakatare Janar na MDD (Antonio Guterres) na mika sakon jaje ga iyalan Deby da ilahirin 'yan kasar Chadi da gwamnatin kasar."

A nata bangaren gwamnatin Amirka, bayan ga sakon jaje ga kasar Chadi, ta yi tir da tashe-tashen hankulan da suka yi sanadin rayuka, ta kuma nuna goyon bayanta ga musanyar mulki cikin ruwan sanyi bisa doka. Amma ta bayyana matsayarta na ci gaba da hulda da gwamnatin rikon kwarya.

Gwamnatin Biden ta nemi a mutunta tsarin mulkin ChadiHoto: Andrew Harnik/REUTERS

 Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amirka Ded Price ya ce ."Abin da muke fatan gani shi ne musanyar mulki cikin girma da arziki bisa kundin tsarin mulkin kasar Chardi, muna fatan ganin an kiyaye dokar kasar tare da mutunta ka'aidojinta. Matsayar Amirka ba za ta canja ba ta fuskar mu'amalar diflomasiyya tsakaninta da Chadi, ofisoshin jakadancin Amirka zai ci gaba da aiki.

Faransa ta yi harshen damo a kan Chadi

Shugaban Emmanuel Macron na Faransa da ke zama tsohuwar gijiyar Chadi, ya bayyana alhini rashin hazikin soja da ya yi tsayin daka na tsare mutuncin kasar. Florence Parly da ke zama ministar tsaron Faransa ta ce : "Shugaba Idriss Deby da ke shugabantar G5 Sahel makonni da suka gabata, mutum ne jajirtacce da ya lashi takobin jibge dakarun kasarsa 1,200 a kan iyakoki uku na kasashen Sahel da ke fama da tarzomar 'yan tada kayar baya." 

Soji sun nada Mahamat Idriss Déby Itno a matsayin shugaban rikon kwarya a ChadiHoto: Marco Longari/AFP/Getty Images

Dan mariyagi Deby mai suna Mahamat Deby Itno ya dare kan karagar mulki a matsayin shugaban rikon kwarya, matakin da Roland Marchal mai nazari a cibiyar bincike kan harkokin mulki na kasa da kasa ke cewa " Ba daidai ba ne a wannan nahiyar, kuma na yi imanin cewa yawancin shugabannin kasashen Afirka sun san abin da ke faruwa yanzu a Chadi, na ba wa dansa shugabancin kasar kuskure ne babba."

Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta ce wannan rashi ne da ya shafi nahiyar bakin daya, inda wasu kasashe kamar Nijar da sauran arewacin Afirka ke bayyana fargabar makomar tsaro a yankin. 

 Sai dai Roland Marchal ya yi mamakin matsayin Faransa dangane da abin da ya biyo bayan rasuwar Deby, inda sojoji suka nada dansa a matsayin shugaba na riko.Ya ce "Faransa na cikin rudani saboda ya zama wajibi ta nuna matsayarta da ba zai yu ba. Abin nufi anan shi ne, an yi juyin mulki a Mali inda Faransar ta bukaci a mutunta kundin mulki tare da komawa tsarin dimukuradiyya ga farar hula. An yi juyin mulki a nan Chadin ma tun da dan marigayi shugaban kasar ya karbi madafun iko tare da alkawarin shirya zabe nan da watanni 18, kuma abin mamaki Faransa ta jinjina da hakan."

Macron na shan suka kan rashin sukar juyin mulki bayan rasuwar Idriss DebyHoto: Ludovic Marin/AFP/Getty Images

A nata bangaren kungiyar Tarayyar Turai ta gargadi dukkannin bangarorin kasar da su mutunta hakkin dan Adam a cikin wa'adin watanni 18 da za a yi na mulkin rikon kwarya: Sai dai tuni wasu rahotanni masu karo da juna daga fadar gwamnatin Chadi ke cewa an bindige mukaddashin shugaban bayan wani sabani kan gadon mulki, yayin da wasu rahotanni ke cewa sabon shugaban yana cikin koshin lafiya.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani