1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana shagulgulan jana'izar tsohon shugaban Koriya ta Arewa

December 29, 2011

A Koriya ta Arewa an ayyana Kim Jong Un dan marigayi shugaban kasar a matsayin babban hafsan hafsoshi, kana jagoran jam'iyar kominisancin kasar

In this Thursday, Feb. 17, 2011 photo released by China's Xinhua News Agency, North Korean leader Kim Jong Il's youngest son and a four-star general Kim Jong Un attends a Lantern Festival concert in Pyongyang, North Korea. North Korea held a concert in Pyongyang on Thursday to mark the Lantern Festival of the lunar year of 2011. (AP Photo/Xinhua, Gao Haorong) NO SALES
Kim Jong Un sabon jagoran Koriya ta ArewaHoto: AP

Daruruwan yan kasar Koriya ta arewa suka taru a dandalin tsakiyar babban birnin kasar Pyongyang a bikin jana'izar tsohon shugaban kasar Kim Jong Il. Dansa kuma magajinsa da sauran mayan hafsoshin sojin suka tsaya kan baranda, inda suke kallon yadda al'amura ke gudana. An dai watsa abin da ke faruwa kai tsaye daga gidan talabijin din Koriya ta arewa. Yau dai itace rana ta biyu da ake bikin jana'izar Kim Jong Il, wanda ya mutu sakamakon bugun zuciya a ranar 17 ga watan da muke ciki, kamar yadda hukumomi sanar. A shagugulan da ake yi ne dai aka bayyana dan marigayin Kim Jong Un a matsayin shugaban kasa, babban kwamandan askarawan kasar, kana jagoran jam'iyar komunisanci. An yi tsit na minti uku a dai-dai karfe 12 rana na kasar.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu