1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana shakka ko sabon shugaban Kenya zai aiwatar da manufofi na gari

March 15, 2013

A shekaru baya nan Kenya ta fita daga kasar da ake dangantawa da kyakkyawan mulkin demokardiyya zuwa wadda matsalar cin hanci da rashin adalci ta yi wa katutu.

President elect Uhuru Kenyatta greets his supporters in the company of his wife Margaret soon after attending a church service in his rural home town of Gatundu, north of capital Nairobi, March 10, 2013. REUTERS/Noor Khamis (KENYA - Tags: ELECTIONS POLITICS SOCIETY)
Hoto: REUTERS

A wannan makon ma jaridun sun fi mayar hankali ne a kan sakamakon zaben kasar Kenya. A babban labarinta jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi.

"Sabon shugaban kasar Kenya na amsa wani suna da ya taba zama wani babban buri. A watan Disamban shekarar 1963 Jomo Kenyatta ya jagorancin Kenya ta samu 'yancin kai, abin da aka alakanta shi da fatan kafa wata kasa ta adalci, kawo karshen talauci da ba wa kowa dama iri guda. Sai dai shekaru 50 bayan 'yancin kan haka ba ta cimma ruwa ba. A dangane da tarihinsa ana shakka ko sabon shugaban dake zama da ga Jomo Kenyatta, wato Uhuru Kenyatta zai iya aiwatar da tsohon buri a cikin manufofin gwamnatinsa. Domin iyalan gidan Kenyatta kamar takwarorinsu na tsohon shugaban kasa Daniel Arap Moi suna da hannu a dukkan abubuwan da suka haddasa rashin adalci a Kenya yanzu wato kamar kwace filaye, cin hanci da rashawa da kuma rashin gaskiya a cikin tsarin shari'ar kasar."

Da sauran rina a kaba ga demokradiyyar Afirka

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta fara labarinta ne da cewa zai zama riga malam masallaci idan tun yanzu aka fara magana game da wani sabon zamani a nahiyar Afirka, musamman dangane da bunkasar tattalin arziki, karuwar rukunin mutane masu matsakaicin karfi da kuma karin demokardiyya, sannan sai ta ci-gaba kamar haka.

Kenya ta fuskanci rikici bayan zaben shekarar 2007Hoto: Getty Images

"Ko shakka babu an samu raguwar yake yake a nahiyar Afirka sannan an kafa gwamnatocin fararen hula fiye da shekaru 10 baya sannan a yankuna da dama na nahiyar ana samun bunkasar tattalin arziki, abin da ma ya sa wasu ke kwatanta Afirka da sabuwar Asiya. Sai dai wani koma baya ga kyakkyawan fatan da ake wa nahiyar ya fito ne daga wata kasa wadda aka dade ana wa kallon daya daga cikin kasashen nahiyar da ke cin gajiyar mulkin demokradiyya da bunkasar tattalin arziki. Da wani karamin rinjaye al'umar Kenya sun zabi wani shugaba da zai gurfana gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya dake birnin The Hague. Ana tuhumar Uhuru Kenyatta da hannu a rigingimun da suka biyo bayan zaben shekarar 2007 da suka yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 1000."

Sabuwar yarjejeniya tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu

Gwamnatocin biranen Khartoum da Juba sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya game da mai do da aikin tura danyan mai na Sudan ta Kudu ta bututan mai da suka ratsa ta kasar Sudan, a ma halin da ake ciki Sudan ta Kudu ta fara janye dakarunta daga yankin kan iyakar kasashen biyu, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung.

Omar al-Baschir (dama) da Salva KiirHoto: KHALED DESOUKI/AFP/Getty Images

"Bayan amincewa da wannan yarjejeniyar da Sudan da kuma Sudan ta Kudu suka yi a birnin Addis Ababa a wannan makon, kasashen biyu sun kuma rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi da za su daidata batun shata kan iyakokinsu da suke takaddama kai da kuma batun hadin kan tattalin arziki tsakaninsu. Sai dai kamar a da har yanzu ba a cimma daidaito game da yankin kan iyaka na Abyei ba, an dage tattauna wanna batu har zuwa watan Satumba. Haka zalika kasashen biyu na ci-gaba da zargin juna da tallafa wa kungiyoyin tawaye dake cikin kasashen su. Wannan kuwa inji jaridar na saka ayar tambaya game ad yarjeniyoyin da aka cimma kawo yanzu. A mako mai zuwa ne Khartoum da Juba za su sake komawa kan teburin shawarwari a wani sabon yunkuri na daidaita tsakani."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman