1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKoriya ta Kudu

Koriya ta Kudu: Lee Jae-Myung na kan gaba da yawan kuri'u

June 3, 2025

A Koriya ta Kudu dan takarar jam'iyyar masu ra'ayin kawo sauyi Lee Jae-Myung shi ne ke kan gaba a zaben shugaban kasar da tazarar mai yawa,

Südkorea Seoul 2025 | Wahlkampfkundgebung von Lee Jae-myung vor Präsidentschaftswahl
Hoto: Daniel Ceng/Anadolu Agency/IMAGO

A cewar wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da gidajen talabijin suka fitar bayan rufe rumfunan zabe.Mista Lee ya samu kashi 51.7% na kuri'un da aka kada, yayin da abokin hamayyarsa Kim Moon-soo mai ra'ayin mazan jiya ya samu kishi 39.3%.

Lee Jae wanda lauya ne  ya kasance magajin garin Seongnam daga 2010 zuwa  2018, sannan gwamnan lardin Gyeonggi har zuwa 2021.