Ana shirin yi wa gwamnatin Madrid bore
November 3, 2017Talla
Majalisar dokokin Kataloniya, ta yi kira ga al'umar yankin da su fito su yi zanga-zangar adawa da fara gurfanar da manyan jami'an gwamnatin yankin da mahukuntan Madrid suka yi. A wani sako ta shafin Twitter, majalisar ta ce mahukuntan Madrid ba su isa tilasta mutane masu 'yanci yin shiru ba.
Bayanai na nunin cewa akwai wasu kungiyoyi a Kataloniyar da suka shirya gangamin adawar ranar 12 ga wannan wata na Nuwamba, baya ga wani yajin aiki na gama-gari da gamayyar kungiyoyin kwadago suka kira a ranar takwas ga wata. Kiraye-kirayen dai na zuwa ne yayin da kotun kasar Spaniya ke shirye-shiryen kama tsohon shugaban yankin Carles Puigdemont wanda a halin yanzu yake a kasar Beljiyam.