Ana shirye shiryen zabe a Mali
February 18, 2013 A cikin watan Yulin nan mai zuwa ne,kasashen duniya suka yi amanan cewar kasar ta Mali zata iya shirya zabubukanta na gama gari da suka hada da na shugaban kasa,hadi da na 'yan majalisar dokoki sannan da na kananan hukumomi a lokaci guda domin baiwa kasar damar komawa a kan tafarkin demokradiya bayan sojojin kasar sun kifar da gwamnatin Amadou Toumani Touré.
Tun dai bayan juyin milkin da ya kara jefa kasar cikin wani mawuyacin hali,duniya ta zuba ido jiron ganin an sake gudanar da zabubukan wadanda tun can farko aka tsaida watan Aprilu domin zaben shugaban kasa bayan wa'adin milkin hambararen shugaban.
To saidai yanayin da kasar ta tsintsi kanta a cikin na saka shakku sosai ga gudanar da zabubukan a cikin kankanen lokaci. Barista Mamadou Ismael Konaté,daya daga cikin mambobin kungiyoyin fararen fulla a kasar ta Mali,ya nuna shakkunshi ga zaben da ake son shiryawa nan da watani 5 masu zuwa,inda yace
"Ya ce tunanin shirya zabeb shugaban kasa,da na majalisar dokoki hadi da na kananan hukumomin cikin wannan hali,abu ne dake bukatar natsuwa da kimtsi daga hukumomin rikon kwarya na kasar Mali ta hanyar tsara komai ya zo yadda ake bukata,sannan su baiwa 'yan takara damar ziyara a cikin kasa tare da amnucewar kowa ga sharudan da za shinfidawa."
Dama dai tun can farko kungiyar tattalin arzikin kasashen ecowas da ma tarayyar turai,sun sha nanata bukatar ganin an hazarta kwato arewacin kasar ta Mali daga hannun kungiyoyin da suka kafa sayyu a arewacin kasar sannan kuma kasar ta gaugauta shirya zabubuka domin mayarda tafarkin demokradiya da kuma martabar wannan kasar da a can baya akwa kallon wani madubin demokradiya ga sauran kasashen afrika.
To amman a yayin da wasu ke nuna shakkunsu ga kawarin gwiwar kasar gurin shirya zaben,wasu na ganin hudda rana da aka yi zai taimakawa ga matsa kaimi ga hukumomin wuccin gadin gurin daidaita al'amura inji Soumaila Cissé daya daga cikin 'yan siyasar kasar wanda ya taba shan kaye a zaben baya baxan nan da aka gudanar a shekara ta 2007.
" Idan an samu magance matsalar arewaci ta hanyar soji,a koma kuma ga hanyar demokradiya,domin akwai kalubale da dama,da suka hada da shirya rejistan zabe,da kuma baiwa 'yan kasar damar shiga takara kama daga arewaci zuwa kudancin kasar,sannan an maido wadanda suka kauracewa garuruwansu,to amman ina tsammanin tsaida rana zai taimakawa a shiga gadan gadan cikin sha'anin"
Alkaluman majalisar Dinkin Duniya dai sun yi amanin cewar kimanin mutane dubu dari 3 da 80 ne suka bar muhalinsu ya zuwa kasashe makwabta yayinda sama da dubu 150 ne suka baro arewacin kasar tun farkon barkewar rikicin.
To amman shi barista Mamadou Ismael Konaté na ganin muddun akwai wani sashe na 'yan kasar da baza su iya cika nauhinsu ba na 'yan kasa gurin kada kuri'a,to fa ba za a samu nasarar zaben ba.
"Idan har akwai wasu 'yan kasar da baza su shiga zaben ba,to zabe ne da zai fuskanci matsala ta inganci da ma adalci,to amman da yake har yanzu muna da sauran lokaci ,ina sa ran gwamnatin Mali da sauran 'yan kasar zasu yi iya kokarin sun warware wannan matsalar domin mu gudanar da zabubuka cikin tsanaki da yarda"
Koda yake Soumaila Cissé ,yace bukatar dara dai kasawa ,muddun aka amunce da sakamakon zaben to komi ya kare.
"Babban abu mai mahimmanci shi ne zaben ya kasance mai inganci ne,kuma amuntacce daga jama'a,yadda za a samu hukumomi amuntattatu daga 'yan kasa wadanda za su ci-gaba da gudamnar da ayukan ci gaban al'umma."
Abun jira a gani dai shi ne yadda hukumomin kasar zasu samu shirya jerin zabubukan a cikin kankanen lokaci duk kwa da halin da kasar ke ciki.
Mawallafa: Sandrine Blanchar/ Issoufou mamane
Edita: Mohammad Nasiru Awal