SiyasaAustraliya
Ana ta farautar mutumin da ya kashe 'yan sanda a Australia
August 28, 2025
Talla
Rundunar 'yan sandan Australia ta ce ba za ta gajiya ba, a kokarinta na ci gaba da farautar wani 'dan bindiga da ya nausa cikin daji, bayan halaka jami'anta biyu tare da jikkata daya a ranar Talata.
'Yan sandan sun fantsama cikin wani surkukin dajin garin Porepunkah na jihar Victoria, da ke yankin arewa maso gabashin kasar.
Karin bayani:Fasinjoji sun tsallake rijiya da baya a Australia
Jami'an tsaron kasar sun ayyana Dezi Freeman mai shekaru 56, a matsayin wanda ya aikata wannan tabargaza, sannan ya ruga cikin dajin dauke da miyagun makamai a hannunsa, kuma ya yi fice wajen kwanton bauna a daji.