1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana tattara sakamakon zabe a Ghana

December 7, 2024

Al'ummar Ghana sun kammala kada kuru'un zaben sabon shugaba da kuma 'yan majalisun dokoki. Ghana dai kasa ce ta yammacin Afirka da ake yaba wa tsarin tafiyar da dimukuradiyyarta.

Zaben kasar Ghana na 2024
Zaben kasar Ghana na 2024Hoto: Julius Mortsi/ZUMAPRESS/picture alliance

Rahotannin da ke fitowa daga kasar Ghana na cewa an rufe rumfunan zabe a wannan yammaci, bayan kammala zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da aka yi da ranar yau Asabar. Bayanai dai sun nunar da cewa an samu karancin fitar masu kada kuri'a a zaben

Takara dai ta fi zafi ne a tsakanin mataimakin shugaban kasa Mahamudu Bawumia na jam'iyyar NPP da kuma tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama na jam'iyyar NDC.

Mutane miliyan 18 da dubu 700 ne suka yi rajistar zaben na Ghana, a kasar da ke da tarihin gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali a yankin yammacin Afirka.

Akwai dai kujerun 'yan majalisar dokokin kasar guda 276 da ake fafatawa a ranar ta Asabar.