1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaFaransa

Faransa na tattauna rikicin Gaza da kasashen Larabawa

Abdoulaye Mamane Amadou
May 24, 2024

Kasar Faransa na karbar bakwancin wasu jiga-jigan kasashen yankin Larabawa da zummar tattauna batutuwan yankin Gabas ta Tsakiya musamman ma yakin Gaza.

Hoto: Ludovic Marin/AP Photo/picture alliance

Faransa ta barbi bakwancin wasu jiga-jigan kasashen Larabawa ciki har da Firaministan Katar da ministan harkokin wajen Saudiyya da na Jodan da Masar don tattauna batun halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya musamman ma rikin Gaza.

Karin bayani : Martani game da karar Afirka ta Kudu kan Isra'ila

Fadar Elysée ta sanar cewa shugaba Emmanuel Macron zai tattauna da masu fada ajin ne kan fafutikar da kasashen duniya ke yi na ganin an cimma yarjejeniyar sulhu a yakin da Isra'ila ke yi a Gaza.

Karin bayani : Kotun ICC ta bada sammacin kama Netenyahu da jagororin Hamas

A nashi bangare ministan harkokin wajen Masar Ahmad Abou Zeid, ya ce manufar taron shi ne na duba yiwuwar hanyoyin shigar kayayakin agaji ayankin Gaza da batun da ke daukar hankali a yanzu na samar da kasashen Isra'ila da ta Falasdinawa don samun dawamammen zaman lafiya.