Ana tattaunawa kan nukiliyar Iran
June 17, 2014Talla
Kasar Iran da kasashen Yamma da ke halartan tattaunawa kan sasanta batun makamashin kasar sun fara wani zagayen tattaunawa. Shugabannin suna lalubo hanyar da za bi domin samun matsaya, ta yadda za a kawo karshen takaddamar mallakar nukiliyar kasar Iran
Kungiyar Tarayyar Turai ke jagorantar tattaunawa, inda ake sa ran sassautowa daga kowane bangare yayin da aka zo rubuta tankardar karshen ganawar, wadda ke babban cikas da ake samu.
A yanzu haka wasu kasashen yamma sun fara sassautawa kan adawar da suke nuna wa Iran, inda tuni kasar Birtaniya ta sanar da sake bude ofishin jakadancin kasar ta Iran, wanda ke nuna aluman yarda da juna tsakaninsu da Iran.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Suleiman Babayo