1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana wani bincike kan Shugaba Trump

April 4, 2019

Majalisar dokokin Amirka ta bukaci hukumar haraji ta kasar da ta mika mata cikakkun bayanan harajin da Shugaba Donald Trump ya biya cikin shekaru shida da suka gabata.

USA, Washington: Treffen zwischen Pence, Trump und Fabiana Rosales
Hoto: Reuters/C. Barria

Shugaban kwamitin da ke kula da harkokin haraji a majalisar ta Amirka, Richard Neil, wanda ya mika bukatar a hukumance, ya kuma bukaci harajin kamfanoni mallakin Mr. Trump na tsawon shekarun shida.

Hakan mataki ne da ya zo yayin da 'yan jam'iyyar Demoracts a majalisar ke karin haske kan harkokin kudade da suka shafi shugaban na Amirka.

Wannan ne dai karo na farko bayan 45 da majalisar ke neman cikakkun bayanan da suka shafi shugaban kasa a Amirka.

Majalisar ta bayar da wa'adi ne na mako guda ga hukumar harajin kasar kan wannan bukata.