Ana zabe karo na uku a Isra'ila
March 2, 2020Talla
Wannan ne dai karo na uku da ake zabe cikin kasa da watanni 12 a Isra'ilar, kuma makonni biyu gabanin shari'ar da ke gaban Mr. Netanyahu da ke fuskantar zarge-zarge na cin hanci da rashawa.
Ana sa ran a zaben da mutane miliyan shida da dubu 400 za su kada kuri'a, takara za ta yi zafi tsakanin jam'iyyar Likud da ta Blue and White, inda kowane bangare ke nuna alamun da wuya ne ya yi galaba da wani rinjaye a majalisar kasa.
Ko a zaben kasar da aka yi a watannin Afrilu da Satumbar bara ma dai, babu wata jam'iyyar da sami rinjaye kai tsaye.