1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zaben kasa a Australia

May 21, 2022

Ana gudanar da zaben majalisar dokokin kasar Australia, zaben da ake ganin takara za ta yi zafi tsakanin jam'iyyar Conservative ta Firaminista Scott Morrison da Labor ta adawa.

Parlamentswahl in Australien | Scott Morrison Liberale Partei
Hoto: MICK TSIKAS/AAP/IMAGO

An bude rumfunan zabe a sassa daban-daban na kasar Australia, inda 'yan kasar za su zabi 'yan majalisar kasa.

Ana dai sa ran samun sakamakon da zai iya zama kusan kan-kan-kan, kuma ta yiwu jam'iyyar adawa ta Labor ta ba da mamaki kamar yadda kuri'ar jin ra'ayi ya nunar.

Jagoran adawar kasar ta Australia Anthony Albanese ya yi kiran da a juya wa Firaminista Scott Morrison baya, yana mai bayyana shi da mai manufofi na raba kan kasa.

Sama da mutum miliyan 17 za su kada kuria'a, inda za su zabi 'yan majalisar wakilai 151 da kuma 'yan majalisar dattawa 78.

Tuni ma dai fiye da rabin wadanda suka cancanci zabe suka riga suka kada kuri'arsu kafin wannan Asabar.