An tsaurar tsaro yayin zabe a Iraki
October 10, 2021Talla
Zaben na zuwa ne kwanaki biyu bayan da 'yan kasar suke tunawa da 'yan fafutuka kusan 600 da aka kashe a lokacin zanga-zangar adawa da rashin adalcin shugabannin gwamnati.
Rundunar sojin Iraki ta jibge jami'an tsaro sama da 250,000 don hana aukuwar hare -haren ta'addanci, an kuma rufe filin sauka da tashin jiragen sama da ke Bagadaza har sai bayan zabe. Ana sa ran samun sakamakon farko na zaben a ranar Litinin.
Kasar wacce ta dogara da arzikin man fetur, na fuskantar rikicin siyasa da matsin tattalin arziki mai zafi, matakin da sa 'yan kasar suka fara zanga-zangar gama gari a 2019.